Gurbin Naƙasa a Cikin Karin Maganar Hausawa

    Abstract

    Proverb is one sense statements in Hausa; it takes someone longtime to achieve something. Life is a mixture of sweetness as well as bitterness; scholars are saying life of an individual would not be complete until he/she comes to an end. This paper titled place of disability in Hausa proverb, aims to bring out proverbs that are in relations with disability in Hausa literature and to rescue these proverbs from extinction. The objectives of this paper are to show to the world how Hausas use proverbs that have relationship with disability in their daily activities. This paper applied interview and the used some related books on disability in gathering data. However, the paper gives more light on Hausa proverbs and proverbs that are mainly on disability in order to express sense statements in an aspect of language and literature of Hausa. Finally, the paper found that, Hausa has verse sense statements, where it touches all aspect of human endeavor. This paper also found out that, some disabilities are inborn people inherited them from their forefathers, while some are as a result of accidence.

     

     

     

    Keywords: Disability, Hausa, literature, place, proverb

     

    Tsakure

    Karin Magana yana daga cikin zantukan hikimar Hausawa. Sannan kuma ai ba a yabon ɗan kuturu sai ya mutu da yatsunsa. Kasancewar rayuwar duniya juyi-juyi ce, yau ana lafiya gobe kuma wata larurar takan iya aukuwa. Masu hikimar Magana sukan ce halittar mutum ba ta cika sai ranar da ya bar duniya (mutu). Saboda haka ne, wannan takarda mai taken: Gurbin Naƙasa a Cikin Karin Maganar Hausawa, ta yi nazarin maʼanar naƙasa da dalilan da sukan sanya naƙasa da misalanta. Haka nan, ta yi ƙarin haske game da karin maganar Hausawa, kuma ta tsamo wasu karin Magana masu alaƙa da naƙasa, domin nuna irin hikimar da ke tattare a cikin harshe da adabin Hausa. Sannan ta bayyana halin komai da ruwanka da harshen Hausa yake da shi, na babu ɓangaren da bai taɓo ba na daga rayuwar mutane. Manufar wannan takarda ita ce zaƙulo karin maganar da suke cikin adabin Hausa masu dangantaka da naƙasa, tare da taskace su maganin salwanta, dominʼyan baya su amfana. Maƙasudin Bincike kuwa, shi ne wajjahar wa duniya irin hikimar da Hausawa suke da ita wurin amfani da karin Magana masu dangantaka da naƙasa a cikin zantukan suna yau da kullum. Sannan an yi amfani da binciken littattafai masu dangantaka da wannan aiki a cikin ɗakunan karatu. Haka nan, an tattauna da masu larurar naƙasa daban-daban, domin samun ƙarin haske game da wasu karin maganan. Sannan takardar da jero karin maganar Hausawa waɗanda suke da dangantaka da naƙasa. Daga ƙarshe sakamakon binciken ya nuna irin faɗi da hikimar da harshen Hausa yake da suna cewa babu ɓangaren da ya ware a rayuwar mutane ba tare da ya samar masa da matsuguni ba. Haka kuma ya nuna wata naƙasar ana gadonta ne tun wurin iyaye da kakanni ba a nan duniya ake gamuwa da ita ba.

    Fitilun Kalmomi: Adabi, Hausa, gurbi, karin magana, naƙasa.

    DOI: 10.36349/sojolics.2026.v02i02.046

    author/Al-Musawi, I. U., Girei, I. I., & Umar, H.

    journal/Sokoto JOLICS 2(2) | August 2026 |

    Pages